YADDA AKE HADA APK

KODULAR CREATOR: kodular creator shima kamar appybuilder ne saboda shima yana cikin family din drag and drop ne, idan ka iya appybuilder baka da bukatar koyon kodular haka kuma idan ka iya kodular baka da bukatar koyon appybuilder . kusan komai nasu daya ne, sai dai extension ko source code na kodular baya yi a appybuilder hakanan kuma na appybuilder baya yi a kodular kuma ba zaka iya bambancewa ba saboda duka source codes dinsu yana karewa da .aia ne, haka kuma duka extension nasu yana karewa da .aix ne don haka duk wanda ya baka extension ko ka saya to dole ya gaya maka na wane portal ne, saboda idan kayi uploading zai hau portal din amma ba zai yi ba kuma ba zai ce maka wai ba nasa bane ba.

Amfanin kodular da appybuilder kusan duk daya ne, dan bambancin shine kodular yafi dadin sha’ani ga wanda ya fahimce shi, amma appy builder yafi sauki ga dan koyo. Abu na biyu kodular sun fi appybuilder cpc mai kyau. Abu na uku su kodular ba’a iya hada earning app da su wato application wanda baya containing komai sai ads. Shi yasa idan ka kammala app da su to tilas sai kayi requesting for review sun tantance sannan ya fara nuna ads.

Sannan kuma suna da wata illa daya bayan ka gama building apps dinka to tilas ka saurara minimum of 48 hours sannan kayi requesting review amma idan publishing zaka yi a playstore to ba sai jira ba, kawai kayi publishing duk da baya nuna ads din, da zaran ya shiga playstore zai fara nunawa.

Domin jarabawa shiga nan KODULAR

APPYBUILDER: appybuilder ma wani portal ne da ake amfani da shi wajen hada app wanda zaka iya kusan duk wani app da ka sani ta hanyar amfani da shi. Appybuilder da duk sauran portals ire-iren shi ana kiran su drag and drop portals saboda su zaka rika dragging and dropping na feature ne kawai daga baya sai kayi compiling.
Appybuilder ya sha bambam da duka sauran portals din da muka ambata tun daga tsari da yanayi da kuma yanayin aiki. Sannan shi appybuilder kyauta ne ake amfani da shi zaka iya monetizing app din ka fully ta hanyar nuna banner da interstitial ads a app dinka kuma zaka iya customizing package name na app dinka yadda kake so.

AMFANINSU
Kyauta ne gaba daya babu wani subscription.
Zaka iya importing na wani feature wanda basu da shi ta hanyar amfani da extension files.
Zaka iya amfani da souce code kawai kayi editing ka sanya details naka.
Zaka iya publishing app dinka a playstore.
 Suna da saukin sha’ani musamman idan apps din ka masu saukin building ne.

ILLOLINSU
§ Duk earning din ka na google suna da 5% shi yasa ba zaka iya using dinsu ba dole sai da gmail.
§ Idan kana bukatar extension to ba duka bane suke bayarwa free dole ka saya akan kudi mafi karanci dala 10.
§ Suna da low cpc.
§ Wasu apps dinsu google basa yarda ayi publishing dinsu a playstore misali earning apps.
Shiga nan don jarabawa APPYBUILDER

APPYPIE: shima wani portal ne wanda ake creating android apps ko iphone kai har ma da Windows apps su kuma usually suna baka tsawon sati biyu ne ka jaraba amfani dasu a kyauta wanda bayan sati biyun nan ya wuce to ba zaka iya cigaba da amfani da su ba har sai kayi subscription. Gaskiya suna da features masu kyau, zaka iya yin apps masu kyau sama da kala dari masu ban sha’awa.

AMFANINSU
Suna features masu kyau don features dinsu yafi na andromo kyau.
Suna supporting different apps kamar irin su website apps, ebook, notebooks da sauransu.
Zaka iya publishing na apps dinsu a playstore.
Suna da push notification feature wanda zaka iya tura ma duk wanda yayi installing na app dinka message. Wannan feature din sune kadai suke das hi a duk cikin portals da muka lissafa.

ILLOLINSU
Suna da yar wuyar sha’ani ga dan koyo ba kamar appsgeysa da andromo ba.
Site dinsu is not mobile friendly, ma’ana idan ba da PC kake using ba to gaskiya zai rika yi maka slow ne

Ku shiga nan don jarabawa APPSGEYSER

: andromo yana cikin manya kuma shahararrun portals da ake amfani da su wajen creating applications irin na wakoki, ebooks, website, rubutun zube da sauransu. Kusan ince kowa zai iya developing application a Andromo. Da farko zaka yi register da su, daga nan zasu baka dama kayi creating application daya don kaga yadda suke da saukin sha’ani. Bayan kayi creating wannan app din kwara daya ba zasu baka dama ka sake creating wani ba har sai kayi subscription da su saboda su services nasu ba kyauta bane. Zaka rika biyansu akalla dala 8 duk wata kuma basa accepting subscription na wata daya, karanci shekara daya ne. kaga kenan zaka yi lissafin dala takwas sau 12 sune adadin kudin da zaka biya su don more amfani da portal nasu.

AMFANINSU
Suna da matukar saukin sha’ani.
 Zaka iya amfani da emails daban-dban don sake register don more garabasar app daya da suke bayarwa.
Shi app dayan zaka iya updating dinsa ta hanyar cire content dinsa kacokan ka sanya wani content din.
Apk dinsu is highly compressed bjarabawa nauyi ba.
Apps dinsu yana da cpc mai kyau.

ILLOLINSU
Idan baka yi subscription da su ba, to ba zasu baka damar sanya admob ad units dinka ba.
Basa karbar subscription na wata daya sai akalla ya kai na shekara.
Suna sanya watermark a free apps dinsu, wato alamar cewa a wajen su ne kayi app din.
Idan subscription dinka na dala 8 ne a wata to ba zaka iya customizing package name naka yadda kake so ba.
Shiga nan don jarabawa

YADDA AKE SAWA FACEBOOK SECURITY system

wani tsarine da facebook suka bawa masu amfani da shafinsu wata dama wanda xaka kare facebook dinka ta hanyar sanya masa security shi wannan tsari yana da matukar dadi sannan kuma yana da mungun hadari domin kuwa dakayi active na wannan tsarin to facebook xasu turoma da text wanda yake dauke da security wannan security to shine abu mai muhimmanci wanda da shine idan kayi login na account din to xa,a umar ceka kasa pin dinka to dole saikasa wannan security sannan xai bude to ka ga kwa babu dama wani yahau fb dinka domin idan yahau xasu umarci yasa pin to matsalar sa kuma shine idan har ka manta wannan security da suka baka to sai ince ta karema domin babu dama kahau fb dinka saide yanxu koda ka manta paswod din idan kahau wata operar kayi login to xasuyi text xuwa number ka da new security to sai kaje kasahi sannan ya bude Ina sake nana ta muku yana da hadari da xarar ka seta idan sim din ya bata to babu kai babu hawa facebook Sabo da haka akiyaye to baride mu fara bayanin kaje facebook dinka ta opera ka budeshi sannan kayi chan kasa xakaga inda aka rubuta to saika shiga nan idan ya bude xakaga abubuwa A Jere Kamar Haka …… GENARAL SECURITY PRIVESY TIMELINE & TAGGING BLOCKING NOTIFICATION TEXT MESSAGING To Kawai Saika Shiga Idanya Bude To Zakuga kai tsaye ya bude muku wuri kamar haka … inda Idan Kuka Lura Zakuga Jerin Sunaye Guda Uku Na Farko .. 1= Text message login Code .. Enable 2= Login Notification code .. Enable 3= Login Aproval ON .. Enable To Anan Abinda Ake Bukata Shine Duka Anason Sai Mun Maida Enable ta koma Deable.. Tashin Farko Domin Saita na tsakiya domin shiyafi saukin saiti watoEmail Notification login Code kawai saika danna kalmarEnableinda zakaga nan take ta canja kanta daka enable zuwa kalmar Disable.. Amfanin saita wannan kuwa shine Aduk lokacin da wani hatsa bibi yayi yunkurin hawa Facebook dinka tonan take Facebook zasu sanar dakai ta hanyar sakon message zuwa Akwatin email dinka … Suma sauran su Text message login code da Login Aproval to suma haka xaka musu wato ka maidasu dan enable xuwa denable idan kayi haka shikkenan duk lokacin da wani yayi kokarin hawa account dinka to xasu sanar dakai cewa xa a hau fbok dinka da opera kaxa da waya kaxa kuma a time kasa sannana xasu turoma da wani new security domin ka yi amfani dashi kuma ko kaine xakahau fb din naka a wata wayar to sai sun ma hakan Allah ya bada sa,a

BAN_BANCIN BLOG DA WEBSITE

Bambance-bambancen Da Ke Tsakanin Shafin Yanar Gizo Da Shafin Blog
Babban abin da ya bambanta daskararren shafi da kuma shafin blog shi ne yanayin yadda bayanan shafin ke kasancewa. Shi shafin blog kan kunshi bayanai ne a bisa tsarin daya na-biye da daya, sabon bayani a saman tsohon bayani, sannan kowanne na dauke da lokaci ko kwanan watan da aka wallafa shi da kuma sunan wanda ya wallafa shi. Yayin da shi kuwa daskararren shafi, bayanan sa tsayayyu ne a bisa tsarin da maginin shafin ya gina su. Idan ana son sauya su, to za a tuntubi maginin shafin ne domin sai an bukaci yin gyara ko kari a cikin kod din da aka gina shafin da shi. Anan, za a iya fahimtar cewa shafin blog na saukaka wa mai shi daman wallafa sababbin bayanai da kan shi, ba tare da sai ya nemi taimako daga wani masani kan yadda ake gina shafin yanar gizo ba.

Haka kuma, mafi yawanci, akan samu wajen yin sharhi ko tsokaci ("comment") a kan kowane bayanin (kasida) da aka wallafa a shafin blog, abin da ke da matukar wuya a samu a daskararrun shafuka.

Sannan sau da yawa a shafin blog, an fi saukin samun mashigan tura duk wani kasida da aka samu daga shafin zuwa wasu shahararrun zaurukan zumunta irin su facebook da twitter, don gayyatan 'yan'uwa da abokai zuwa shafin da aka wallafa kasidan.

Kammalawa - Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata a Lura:
Duk wanda ya karanta bayanan da na kawo a sama, cikin nutsuwa, zai iya fahimtar cewa: shafin yanar gizo da shafin bulog kusan duk abu daya ne. Sai dai shi shafin blog kawai wani nau'i ne daga cikin nau'ukan shafin yanar gizo.

Don haka, ana iya kiran kowane shafin bulog da sunan "shafin yanar gizo" tare da lura da cewan nau'in sa shi ne "blog".

Ana iya samun shafin yanar gizon da ya kunshi bangarorin biyu, wato bangaren daskararrun shafuka masu kunshe da bayanai tsayayyu, da kuma bangaren blog wanda kan kunshi sababbin mashigai na shafuka masu dauke da sababbin bayanai.

Shawara:
Idan mutum na da burin mallakan shafin yanar gizo musamman na kamfani ko kungiya ko kasuwancin sa, to ina ba shi shawaran cewa ya yi kokari ya nemi kwararren maginin shafin yanar gizon da zai gina masa shafin yanar gizo wanda ya kunshi bangaren daskararren shafi da kuma bangaren blog. Domin hada duka biyun waje guda shi ke bayar da cikakken dama na saka kowane bayani a muhallin da ya dace da shi. Misali, mai shafi zai samu daman jero ayyukan sa ko hajojin sa a wani daskararren shafi da zai iya sanya wa taken "Ayyukan Mu" ko "Hajojin Mu", sannan kuma zai samu daman wallafa jerin sababbin hajoji ko labaran kamfanin sa ko kungiyan sa a wani shafi mai motsi da zai iya sanya wa taken "Blog" ko "Sababbin Hajojin Mu" ko "Meye Sabo?" ko "Labaran Mu" ko "Kasidu" da dai makamantan su.Shafin yanar gizo da kuma shafin blog wasu kalamai ne wadanda kusan duk wani ma'abocin amfani da fasahar intanet ya saba da jin su ko ganin su, sai dai a mafi yawancin lokuta, ba tare da sanin hakikanin ma'anonin su ko bambancin da ke tsakanin su ba. Fahimtan su na da matukan muhimmanci musamman ga wadanda ke son mallakan na su shafin a duniyar gizo. A wannan kasida zan yi kokarin yin takaitaccen bayani ne wanda na ke fatan zai gamsar da duk wani mai son sanin ma'anan shafin bulog da kuma bambancin su da shafin yanar gizo.

Ma'anar Shafin Blog
Shafin blog wanda kalma ne na harshen turanci da ya samo asali daga "weblog", shi ne shiryayyen shafin yanar gizo wanda aka kirkire shi a bisa tsarin da za a iya sabunta shi da bayanai akai-akai, cikin sauki. Ana kirkiran shafin blog ne da wani shiryayyen manhajar yanar gizo na musamman da ke bayar da daman kirkira da kuma gudanar da shafin bulog. Shafukan yanar gizo na mujalla da shafukan yanar gizo masu kawo labarai ko darussa, kaman wannan shafi na Duniyar Sadarwa, su ne misalan shafukan blog, wato su ne ire-iren shafukan da akan kirkire su a bisa manhajar yanar gizon kirkiran bulog.

Magina manhajar yanar-gizo wadanda a turance ake kira "web developers" ko "web programmers" su ne ke iya kirkiran manhajar bulog ta hanyar amfani da sababbin fasahohin zamani na kirkiran shafukan yanar gizo. Akwai kuma kamfanoni daban-daban a duniyar gizo wadanda ke dauke da irin wannan manhajar yanar gizon da ke bayar da daman kirkira da kuma gudanar da shafin blog. Mafi shahara daga ciki su ne: Blogger da Wordpress. Irin wadannan kamfanoni kan tsara manhajar su ne ta yadda idan mutum ya yi rajista a shafin su, zai samu tsararren shafin sa na blog kuma zai samu daman wallafa kasidu ('posts') da kuma yin gyare-gyare a shafin sa na blog din ta wani shiryayyen shafi da akan kira 'control panel' ko 'dashboard' a turance.

Babban dalilin da kan sa a bukaci shafin blog shi ne samun saukin wallafa bayanai na rubuce-rubuce ko fayiloli irin su hotuna da sautuka, akai-akai.

Samuwar fasahar blog a duniya, shi ya bude wa kamfanonin watsa labarai da makamantan su hanyar wallafa labarai a shafin yanar gizo cikin sauki da kuma sauri.

Irin tarin alfanun da fasahar blog ya kawo a duniyar gizo, shi ya janyo samun karbuwan sa ga al'ummomi daban-daban na sassan duniya.

Duk wani shafi da ke duniyar gizo, sunan sa shafin yanar gizo. Don haka Kowane shafin blog shafin yanar gizo ne amma ba kowane shafin yanar gizo ne shafin blog ba.

Wani babban abu da na ke ganin zai saukaka fahimtan bambanci tsakanin shafin blog da shafin yanar gizo, shi ne a sani cewa dole ne duk wani shafi da ke duniyar gizo zai kasance mai nau'i daya daga cikin nau'uka guda biyu na shafin yanar gizo: Shafin yanar gizo mai motsi da kuma shafin yanar gizo mare motsi.

Shafin yanar gizo mai motsi shi ne shafin da aka shirya shi musamman da nufin a rika sabunta shi da bayanai akai-akai, a saukake, kuma a mafi yawancin lokuta, shi ne ake yi wa lakabi da "shafin blog" ("weblog"). Sai dai idan ana batun "shafuka masu motsi" a jimlance, to za a hada har da shafukan sada zumunta irin su twitter da facebook.

Shi kuma shafin yanar gizo mare motsi shi ne shafin da ke dauke da wasu bayanai tsayayyu. Ma'ana ba shafi ne da aka gina shi da nufin a rika sabunta shi da sababbin bayanai akai-akai ba. A kan yi masa lakabi da "daskararren shafi", amma a mafi yawancin lokuta, ba a cika yi masa wani lakabi ba, sai dai kawai a kira shi da "shafin yanar gizo" ("website") tunda shi ne nau'in shafin yanar gizon da duniya ta sani kafin fitowan fasahar bulog.

Counter

YADDA ZAKAYI CONNCTING DIN WLAN, WIFI DA WAYAR KA

YADDA ZAKA YI AMFANI DA WLAN, WIFI NA WAYARKA KO KOMPUTA … Yanzu kamfanonin masu qyara waya sun kai maqura gurin fiddo da waya masu sauqaqa al’amuran yau da gobe, wayoyi masu wifi ko kuma a rubuta wlan wato wireless zasu iya browsing ba tare da layi a jikin wayarsu ba kuma ba tare da modem a komfuta ba kuma duk application me amfani da wireless suma zasuyi aiki da ita kaman opera da whatsapp, 2go da dai sauransu…… Kaman yadda kuka sani wayoyi da dama suna zuwa da wireless musamman wayoyi qirar blackberry, android (ko wace iri), wasu daga cikin symbian da java, windows phone, iPad wato ios kenan… ita wireless ba installing dinta akeyi ba, zuwa take da wayar domin dole se akwai wireless card ko ic a jinkin na’urar me wireless… To yawwa, now we can move on to connect our wireless enable devices… Mataki na farko: ka tabbatar akwai wireless coverage a kusa dakai, ko jami’a, manyan kamfuna, café’s, shoping mall, plaza, da makamantan gurare da akan iya saka wireless router… Idan akwai Wireless : se ka kunna wifi din wayar ka, idan baka sani ko akwai ba, just kunna wifi dinka ita zata fada maka idan akwai wireless ko babu, zata kama available wireless sannan ta fada maka ko open ce ko kuma wep/shared key aka saka mata, Idan open ce: zaka iya connecting ba tare da ka saka password ba, se kayi browsing kyauta, misali abokin ka ya kunna hotspot dinsa kuma be saka password ba, ofisoshi domin ma’aikata suyi amfani da ita… Idan wep ce: to dole se kasan password din, misali café koda ba wep aka rubuta ba zaka samu dai an kulle tad a password, se ka tambaya ina wireless take a area din ko kuma ka duba café ka biya kudi se bude maka… Haka zakayi domin connecting da wireless… Nasan zakace shin mene ne hotspot kuma, ana wata ga wata, ba’a gama fahimtar wireless ban a dauko hotspot… Nasan yanzu ka riga ka fahimci mece ce wifi kuma zaka iya connecting dakan ka… next se musan mene ne wireless hotspot ko usb tethering wacce suke zuwa da waya android ko blackberry latest masu zafi a gari… Hotspot feature c eta kowace android wacce take bada dammar ka kunna ta domin masu wifi a wayarsu su ga wirless dinka da sunan da ka seta mata domin suyi amfani dam b din wayar ka ko kudin da ka wayar ka suyi browsing a tasu wayar ba tare da an taba masu kudi ba, in kaga dama kaima ka saka password. Zaka iya business da wayarka idan tana da hotspot, zaka iya kunnawa masu buqatar internet suyi connecting kuma ka caje su kudi yadda ya kamata, Zaka iya kunna hotspot ne a qarqashin wireless connection cikin setting din wayar ka, idan ka bude se ka nemi tethering and mobile hotspot.. ka bude kaje settings tukunna ka saka mata suna da password, duka wanda zeyi connecting zega sunan da ka saka kuma zega se kai ka bud eta da password din… kada ka fadawa mutane faswod dinka dan idan anyi connecting kai bazaka sani ba balle ka kulle… Hotspot wata abace me kyau wanda kai me amfani da wayar android bazaka buqaci modem ba idan kana da computer, kayi subscribing da layinka sannan ka kunna hotspot din idan computa din tana dashi, koda kuwa komputar ka bata da wifi don’t worry, u can still connect by using the USB Tethering, find a compatible use cable mostly wacce tazo da wayar se ka jona ta a comutan, ka hada wayan ka da computa ta usb kenan… Idan kayi haka se kaje dsame place inda ka kunna hotspot, zaka ga yar box ance USB Tethering, wannan box din zata baka daman tickin dinta ne amma dole se ka hada wayar da koputar ta usb cable me kyau, kana kunnawa ka kalli komputar ka zaka ga network ya kawo, amma dole se ka kunna data connection din wayar ka sanna zata fara browsing….: ask your question related to wifi/hotspot xuwa gobe war haka inshaAllah mun gama amsawa kowa tambayar sa..

YADDA AKE SAWA FACEBOOK SECURITY BAYAN PASSWORD

wani tsarine da facebook suka bawa masu amfani da shafinsu wata dama wanda xaka kare facebook dinka ta hanyar sanya masa security shi wannan tsari yana da matukar dadi sannan kuma yana da mungun hadari domin kuwa dakayi active na wannan tsarin to facebook xasu turoma da text wanda yake dauke da security wannan security to shine abu mai muhimmanci wanda da shine idan kayi login na account din to xa,a umar ceka kasa pin dinka to dole saikasa wannan security sannan xai bude to ka ga kwa babu dama wani yahau fb dinka domin idan yahau xasu umarci yasa pin to matsalar sa kuma shine idan har ka manta wannan security da suka baka to sai ince ta karema domin babu dama kahau fb dinka saide yanxu koda ka manta paswod din idan kahau wata operar kayi login to xasuyi text xuwa number ka da new security to sai kaje kasahi sannan ya bude Ina sake nana ta muku yana da hadari da xarar ka seta idan sim din ya bata to babu kai babu hawa facebook Sabo da haka akiyaye to baride mu fara bayanin kaje facebook dinka ta opera ka budeshi sannan kayi chan kasa xakaga inda aka rubuta to saika shiga nan idan ya bude xakaga abubuwa A Jere Kamar Haka …… GENARAL SECURITY PRIVESY TIMELINE & TAGGING BLOCKING NOTIFICATION TEXT MESSAGING To Kawai Saika Shiga Idanya Bude To Zakuga kai tsaye ya bude muku wuri kamar haka … inda Idan Kuka Lura Zakuga Jerin Sunaye Guda Uku Na Farko .. 1= Text message login Code .. Enable 2= Login Notification code .. Enable 3= Login Aproval ON .. Enable To Anan Abinda Ake Bukata Shine Duka Anason Sai Mun Maida Enable ta koma Deable.. Tashin Farko Domin Saita na tsakiya domin shiyafi saukin saiti watoEmail Notification login Code kawai saika danna kalmarEnableinda zakaga nan take ta canja kanta daka enable zuwa kalmar Disable.. Amfanin saita wannan kuwa shine Aduk lokacin da wani hatsa bibi yayi yunkurin hawa Facebook dinka tonan take Facebook zasu sanar dakai ta hanyar sakon message zuwa Akwatin email dinka … Suma sauran su Text message login code da Login Aproval to suma haka xaka musu wato ka maidasu dan enable xuwa denable idan kayi haka shikkenan duk lokacin da wani yayi kokarin hawa account dinka to xasu sanar dakai cewa xa a hau fbok dinka da opera kaxa da waya kaxa kuma a time kasa sannana xasu turoma da wani new security domin ka yi amfani dashi kuma ko kaine xakahau fb din naka a wata wayar to sai sun ma hakan Allah ya bada sa,a

YADDA KE TURA SAKO TA EMAIL ADDRESS {GMAIL}

A baya, mun yi cikakken bayani game da yadda ake bude sabon adireshin Email na Gmail a wayar hannu. Da fatan duk wanda ba shi da Email na Gmail, a yanzu ya mallaki nasa. Idan kuma akwai

mai tambaya, ko kuma akwai wani abu da ba a fahimta ba game da bayanin da muka yi, to ana iya yin comment.

Yanzu kuma, za mu yi bayani ne a takaice, kan yadda mai amfani da Gmail zai aika sako daga Email din sa zuwa ga wani.

Wannan abu ne mai sauki da ba ya bukatar wani dogon bayani.

Domin aika sakon Email daga Gmail din ka kawai abin da za ka yi shi ne,

* Ka bude gmail din ka (wato ka yi login) tare da email din ka da password ta shafin www.gmail.com .

* Idan ya bude sai ka nemi inda aka sa 'Compose' sai ka danna.

* Zai budo maka wani shafi.

* To, a wajen da ka ga an sa 'To' anan ne za ka rubuta adireshin Email din wanda za ka aika ma sakon.

* Wajen da aka sa 'Subject' kuma a nan ne za ka rubuta 'maudu'in sakon'.

* Sai ka yi kasa, ka rubuta wasikar ka a akwatin da aka tanadar, wato wajen da aka sa 'Message'.

* Da ka gama sai ka danna 'SEND'. Shikenan! Nan take sakon zai tafi zuwa Inbox din wanda ka aika ma.

P

YADDA AKE KIR_KIRAN {TEXTBOX} AKOWANI IRIN BLOG

Akwatin rubutu (ko 'textbox' a turance), wani salo ne da magina shafin yanar gizo kan yi amfani da shi don bai wa masu mu'amala da shafin daman yin rubutu a ciki (domin cike fom) ko kuma daukan rubutu daga ciki a shafin yanar gizon. Kusan duk wani shafin yanar gizo da ke bayar da daman cike wani fom a shafin, to dole zai kasance akwai akwatin rubutu. Misali, idan za a yi sharhi (comment) a kan wannan darasin, ko za a aiko da sako a wannan shafin, to za a yi amfani da akwatin rubutu ne wajen rubuta abin da ake son aikawa, sannan bayan an rubuta sai a latsa maballin aikawan.
Sai dai kamar yadda na ambata a farko, ba a wajen cike fom ko aikewa da sako ne kadai ake amfani da akwatin rubutu ba. A lokuta da yawa, masu tafiyar da shafin yanar gizo ko blog kan bukaci sanya wani rubutu ko kod cikin irin wannan akwatin rubutu don bai wa maziyarta shafin su daman dauka ko kwafe rubutun ko kod din daga ciki a saukake ta hanyar yin "copy" zuwa "clipbord" na manhajar shiga intanet din su, ta yadda daga nan za su samu damar ajiye shi (paste) a inda su ke bukata. Wannan shi ne abin da wannan darasi zai koyar, don amfanar masu tafiyar da shafin yanar gizo ko bulog.

Yadda Za a Kirkiri Akwatin Rubutu a Kowane Irin Shafin Yanar gizo Ko Blog

Ana amfani da wani kod na HTML ne don kirkiran akwatin rubutu a kowane irin shafin yanar gizo ko kuma blog. Ga kod din:
<*p><*textarea cols="20" rows="5"> Rubutun ko kod a nan... <*/textarea><*/p>
Kar a manta: a cire alamun * daga kod din kafin a yi amfani da shi. Sannan a lura da wajen da aka sa " Rubutun ko kod a nan... ", nan za a goge, sai a rubuta abin da ake so ya kasance cikin akwatin.

Yadda Za a Canja Girman Akwatin Rubutun

Ana iya karawa da kuma rage fadi ko tsawon akwatin rubutun zuwa dai-dai yadda ake bukata. Idan an dubi kod din na kirkiran akwatin rubutu, za a ga wajen da aka sacols="20" da kuma rows="5". To wadannan bangarori biyu na nufin fadi da kuma tsawon akwatin rubutun. Don haka idan ana so a canja fadin sai a canja lamban na 20 zuwa wani lamba na dai-dai fafin da ake so. Haka idan ana son canja tsayin akwatin rubutun, sai a canja lamban 5 zuwa wani lamban na dai-dai tsayin da ake so.
Karshen wannan darasin ke nan, sai kuma mun hadu a darasi na gaba da yardan Allah. Amma kafin nan, ina fatan an fahimta kuma an amfana kuma an ji dadin wannan.

YADDA AKE BUDE GOOGLE ACCOUNT {GMAIL}

A Sashin Harkokin Duniyar Gizo

new-google-gmail-inbox.png
Gmail ya na da saukin budewa da kuma karanta sako ko aikawa a wayar hannu. Idan ka na so ka mallaki naka Gmail din a yanzu, to kawai ka bi wadannan matakan.

1- Da farko ka shiga www.gmail.com . Za ka ga wajen da aka sa 'New to Gmail? It's free and easy. Create account'. To sai ka danna 'Create account'.

2- Zai budo maka wajen da za ka zabi sunan kasar ka. (country) da kuma wajen da za ka rubuta lambar wayar ka. To a wajen 'choose country', za ka ga 'change' sai ka danna shi.

select-change.jpg
Zai jero maka haruffa, sai ka zabi harafin da sunan kasar ka ya fara da shi. misali, 'N' idan a Nigeria ka ke ko Niger.

nigeria.png
Bayan ka zabi sunan kasar ka, zai dawo da kai wajen da za ka saka lambar wayar ka. To sai ka dan yi kasa kadan, sai ka rubuta lambar wayar da ka ke kan amfani da shi a wayar ka a yanzu. Sai ka danna 'Next'.

3- Za su aiko sakon SMS ga lambar da ka sa, cikin yan mintunan da basu wuce 15 ba. Sai ka dan jira kadan, da zaran sakon ya shigo, sai ka je inbox din ka, ka bude. A cikin sakon, za ka ga wani adireshi (link), sai ka latsa wannan link din. Ko kuma ka kwafe shi, sai ka je browser din ka, ka shiga ta ciki.

4- Bayan ka latsa link din, ya bude, za ka ga wani fom da za ka cike sunan ka (first name), sunan mahaifi (last name) ranar haihuwa (date of birth), da kuma jinsi (gender). Bayan ka cike, sai ka danna 'Next'.

5- Zai budo maka wajen da za ka zabi 'Username' din ka wato sunan da zai zamo adireshin Email din ka. Za ka ga sun baka wasu misalan sunayen adirishin da za ka iya zaba a kasa. Idan kuma wani daban ka ke so, ba daga cikin wadannan da suka baka ba, to sai ka rubuta wanda ka ke so. Da ka rubuta sai ka danna 'Next'. Amma idan akwai wani mai irin wannan sunan, to za su ce bai karbu ba. Ka sake canza wani.

6- Zai budo maka wani shafi da za ka saka mabudin ka na sirri (password). Sannan ka sake maimaita shi a kasa (retype password). Sai ka danna 'Finish'. Shi kenan! Ka gama bude sabon adireshin E-mail din ka na Gmail!

A lura cewa, yana da kyau a yi amfani da browser na Opera-mini ko kuma ainihin browser na wayar yayin yin wannan rajista. Amma ba Uc-browser ba.
Bi wadannan matakai guda shida da muka kawo a yanzu ciki nutsuwa, domin bude sabon adireshin e-mail din ka/ki na Gmail daga wayar hannu.

Idan akwai tambaya sai a yi comment!

BAN_BANCIN BLOG DA WEBSITE

Bambance-bambancen Da Ke Tsakanin Shafin Yanar Gizo Da Shafin Blog
Babban abin da ya bambanta daskararren shafi da kuma shafin blog shi ne yanayin yadda bayanan shafin ke kasancewa. Shi shafin blog kan kunshi bayanai ne a bisa tsarin daya na-biye da daya, sabon bayani a saman tsohon bayani, sannan kowanne na dauke da lokaci ko kwanan watan da aka wallafa shi da kuma sunan wanda ya wallafa shi. Yayin da shi kuwa daskararren shafi, bayanan sa tsayayyu ne a bisa tsarin da maginin shafin ya gina su. Idan ana son sauya su, to za a tuntubi maginin shafin ne domin sai an bukaci yin gyara ko kari a cikin kod din da aka gina shafin da shi. Anan, za a iya fahimtar cewa shafin blog na saukaka wa mai shi daman wallafa sababbin bayanai da kan shi, ba tare da sai ya nemi taimako daga wani masani kan yadda ake gina shafin yanar gizo ba.

Haka kuma, mafi yawanci, akan samu wajen yin sharhi ko tsokaci ("comment") a kan kowane bayanin (kasida) da aka wallafa a shafin blog, abin da ke da matukar wuya a samu a daskararrun shafuka.

Sannan sau da yawa a shafin blog, an fi saukin samun mashigan tura duk wani kasida da aka samu daga shafin zuwa wasu shahararrun zaurukan zumunta irin su facebook da twitter, don gayyatan 'yan'uwa da abokai zuwa shafin da aka wallafa kasidan.

Kammalawa - Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata a Lura:
Duk wanda ya karanta bayanan da na kawo a sama, cikin nutsuwa, zai iya fahimtar cewa: shafin yanar gizo da shafin bulog kusan duk abu daya ne. Sai dai shi shafin blog kawai wani nau'i ne daga cikin nau'ukan shafin yanar gizo.

Don haka, ana iya kiran kowane shafin bulog da sunan "shafin yanar gizo" tare da lura da cewan nau'in sa shi ne "blog".

Ana iya samun shafin yanar gizon da ya kunshi bangarorin biyu, wato bangaren daskararrun shafuka masu kunshe da bayanai tsayayyu, da kuma bangaren blog wanda kan kunshi sababbin mashigai na shafuka masu dauke da sababbin bayanai.

Shawara:
Idan mutum na da burin mallakan shafin yanar gizo musamman na kamfani ko kungiya ko kasuwancin sa, to ina ba shi shawaran cewa ya yi kokari ya nemi kwararren maginin shafin yanar gizon da zai gina masa shafin yanar gizo wanda ya kunshi bangaren daskararren shafi da kuma bangaren blog. Domin hada duka biyun waje guda shi ke bayar da cikakken dama na saka kowane bayani a muhallin da ya dace da shi. Misali, mai shafi zai samu daman jero ayyukan sa ko hajojin sa a wani daskararren shafi da zai iya sanya wa taken "Ayyukan Mu" ko "Hajojin Mu", sannan kuma zai samu daman wallafa jerin sababbin hajoji ko labaran kamfanin sa ko kungiyan sa a wani shafi mai motsi da zai iya sanya wa taken "Blog" ko "Sababbin Hajojin Mu" ko "Meye Sabo?" ko "Labaran Mu" ko "Kasidu" da dai makamantan su.Shafin yanar gizo da kuma shafin blog wasu kalamai ne wadanda kusan duk wani ma'abocin amfani da fasahar intanet ya saba da jin su ko ganin su, sai dai a mafi yawancin lokuta, ba tare da sanin hakikanin ma'anonin su ko bambancin da ke tsakanin su ba. Fahimtan su na da matukan muhimmanci musamman ga wadanda ke son mallakan na su shafin a duniyar gizo. A wannan kasida zan yi kokarin yin takaitaccen bayani ne wanda na ke fatan zai gamsar da duk wani mai son sanin ma'anan shafin bulog da kuma bambancin su da shafin yanar gizo.

Ma'anar Shafin Blog
Shafin blog wanda kalma ne na harshen turanci da ya samo asali daga "weblog", shi ne shiryayyen shafin yanar gizo wanda aka kirkire shi a bisa tsarin da za a iya sabunta shi da bayanai akai-akai, cikin sauki. Ana kirkiran shafin blog ne da wani shiryayyen manhajar yanar gizo na musamman da ke bayar da daman kirkira da kuma gudanar da shafin bulog. Shafukan yanar gizo na mujalla da shafukan yanar gizo masu kawo labarai ko darussa, kaman wannan shafi na Duniyar Sadarwa, su ne misalan shafukan blog, wato su ne ire-iren shafukan da akan kirkire su a bisa manhajar yanar gizon kirkiran bulog.

Magina manhajar yanar-gizo wadanda a turance ake kira "web developers" ko "web programmers" su ne ke iya kirkiran manhajar bulog ta hanyar amfani da sababbin fasahohin zamani na kirkiran shafukan yanar gizo. Akwai kuma kamfanoni daban-daban a duniyar gizo wadanda ke dauke da irin wannan manhajar yanar gizon da ke bayar da daman kirkira da kuma gudanar da shafin blog. Mafi shahara daga ciki su ne: Blogger da Wordpress. Irin wadannan kamfanoni kan tsara manhajar su ne ta yadda idan mutum ya yi rajista a shafin su, zai samu tsararren shafin sa na blog kuma zai samu daman wallafa kasidu ('posts') da kuma yin gyare-gyare a shafin sa na blog din ta wani shiryayyen shafi da akan kira 'control panel' ko 'dashboard' a turance.

Babban dalilin da kan sa a bukaci shafin blog shi ne samun saukin wallafa bayanai na rubuce-rubuce ko fayiloli irin su hotuna da sautuka, akai-akai.

Samuwar fasahar blog a duniya, shi ya bude wa kamfanonin watsa labarai da makamantan su hanyar wallafa labarai a shafin yanar gizo cikin sauki da kuma sauri.

Irin tarin alfanun da fasahar blog ya kawo a duniyar gizo, shi ya janyo samun karbuwan sa ga al'ummomi daban-daban na sassan duniya.

Duk wani shafi da ke duniyar gizo, sunan sa shafin yanar gizo. Don haka Kowane shafin blog shafin yanar gizo ne amma ba kowane shafin yanar gizo ne shafin blog ba.

Wani babban abu da na ke ganin zai saukaka fahimtan bambanci tsakanin shafin blog da shafin yanar gizo, shi ne a sani cewa dole ne duk wani shafi da ke duniyar gizo zai kasance mai nau'i daya daga cikin nau'uka guda biyu na shafin yanar gizo: Shafin yanar gizo mai motsi da kuma shafin yanar gizo mare motsi.

Shafin yanar gizo mai motsi shi ne shafin da aka shirya shi musamman da nufin a rika sabunta shi da bayanai akai-akai, a saukake, kuma a mafi yawancin lokuta, shi ne ake yi wa lakabi da "shafin blog" ("weblog"). Sai dai idan ana batun "shafuka masu motsi" a jimlance, to za a hada har da shafukan sada zumunta irin su twitter da facebook.

Shi kuma shafin yanar gizo mare motsi shi ne shafin da ke dauke da wasu bayanai tsayayyu. Ma'ana ba shafi ne da aka gina shi da nufin a rika sabunta shi da sababbin bayanai akai-akai ba. A kan yi masa lakabi da "daskararren shafi", amma a mafi yawancin lokuta, ba a cika yi masa wani lakabi ba, sai dai kawai a kira shi da "shafin yanar gizo" ("website") tunda shi ne nau'in shafin yanar gizon da duniya ta sani kafin fitowan fasahar bulog.

MENENE BLOG

wannan tutorial din zamuyi bayanin yadda ake bude BLOG daga kamfanin google, wanda akafisaninta da blogger. Kuma zamuyi bayanin menene BLOG, kuma da amfaninshi.

Menene BLOG?
BLOG yana nufin wani shafi, ko wani guri, komuce wani ajine da mutane musamman masana harkar gina shafin yanar gizo, suke budewa, domin suna rubuta makalu(Articles), ko mujallu(Magazines), ko labaru(News update). Haka nanma wasu masana kamar malaman kwalejoji, da jami'o'i wato Lakcarori(Lecturers), suke budewa, domin suna koyarda wasu darrusa, na musamman, hade da hoto ko bidiyo, da sautin murya. Ganin cewa yanzu duniya, mafi yawanci wasu harkoki sunkoma kacokan ta internet, yasa mutane, ko kamfanoni dakuma wasu kungiyoyi, ko jam'iyun siyasa, suke bude BLOG, domin tallata hajarsu, ko watsala labarai, kokuma tallata manufofinsu ga jama'a mabiya wannan shafin nasu.

Amfanin BLOG?
BLOG yanada amfanoni dadama, amma bari mukawo koda guda biyar ne daga cikinsu, wanda mutane sukafi azahiri.

Sune Kamar Haka
Labarai
Iimi
Kasuwanci
Siyasa
Entertainment

Bari mudanyi bayaninsu, daya bayan daya, koda atakaicene, yanda mutane zasuyi saurin fahinta da ganewa.

LABARAI
Mafi yawan kafafen watsa labarai, suna amfani da BLOG, domin suna rubuta labaransu, ta yanda jama'a masu sauraronsu, zasuna kai ziyara domin sukaranta wa'annan labarai, harma suna iya ajiye ra'ayinsu, gameda wannan labarin da suka karanta.

ILIMI
Masana, ko muce malamai, masana ilimi suma sukan bude BLOG, domin suna rubuta bayanai, kokuma sakamakon bincike binciken dasukayi. Banda wannan ma, masana sukan bude BLOG domin suna koyar da dalibansu, musamman masu amfani da yanar gizo, darussa dadama.

KASUWANCI
Mafi yawa daga cikin kamfanoni, ayanzu sukanyi amfanida BLOG dan tallata hajarsu, ga jama'a har sukan iya siyar da wasu daga cikin abubuwan dasukeyi tacikinsa. Bayan haka sukanyi amfani da shafin BLOG nasu, domin sutallata guraben ayyuka ga masu bukata, idan suna dasu ta cikin wannan shafin nasu.

SIYASA
A wannan zamani idan muka lura, yan siyasa sun koma amfani da internet domin tallata manufofinsu ga jama'a. Sannan ta hanyar BLOG, masoya wannan dantakarar, kokuma wannan jam'iya. Kuma suna iya turawa wa'ancan yan siyasan ra'ayoyinsu, kuma nan take zasu ga wannan sakon yatafi ga wa'anda suka turawa.

ENTERTAINMENT
Mawaka, da yan wasan kwaikwayo sukan bude BLOG domin kara kusancinsu da masoyansu, kuma sukan tallata sabbin fina finansu, dakuma wakokinsu ta wannan hanyar, sannan mabiya wannan shafin nasu, anan sukan samu damar dakko sabbin hotuna na wannan dan wasa ko mawakin daya bude wannan BLOG din.

Kai! Nima ta hanyar BLOG nake bada gudunmuwata ga jama'a masusan koyan yanda ake abubuwa dadama awaya kokuma a interent.

Daga kamfanin WhatsApp

Kamfanin WhatsApp a watannin baya ya fitar da wani labari da ke cewa adadin masu amfani da manhajar WhatsApp ya kai miliyan dari biyar (500,000,000). Inda a yanzu adadin ya haura zuwa sama da miliyan dari bakwai (700,000,000). A dai-dai lokacin da masu amfani da manhajar na WhatsApp ke ta karuwa a sassa daban-daban na duniyar, wani labari mai kayatarwa ga masu amfani da manhajar na WhatsApp da muka samu a satin da ya gabata, shi ne labarin fitowar sabon tsarin yin kira a WhatsApp din. Masu amfani da WhatsApp da dama a yanzu suna iya kiran junan su kyauta ta hanyar amfani da 'data' na Intanet. Wato dai a takaice, kamar yadda manhajar Viber ya ke. Sai dai kuma masu amfani da WhatsApp a wayoyin Android ne kadai ke da daman samun wannan sabon tsari a yanzu.