Home BAN_BANCIN BLOG DA WEBSITE

Bambance-bambancen Da Ke Tsakanin Shafin Yanar Gizo Da Shafin Blog
Babban abin da ya bambanta daskararren shafi da kuma shafin blog shi ne yanayin yadda bayanan shafin ke kasancewa. Shi shafin blog kan kunshi bayanai ne a bisa tsarin daya na-biye da daya, sabon bayani a saman tsohon bayani, sannan kowanne na dauke da lokaci ko kwanan watan da aka wallafa shi da kuma sunan wanda ya wallafa shi. Yayin da shi kuwa daskararren shafi, bayanan sa tsayayyu ne a bisa tsarin da maginin shafin ya gina su. Idan ana son sauya su, to za a tuntubi maginin shafin ne domin sai an bukaci yin gyara ko kari a cikin kod din da aka gina shafin da shi. Anan, za a iya fahimtar cewa shafin blog na saukaka wa mai shi daman wallafa sababbin bayanai da kan shi, ba tare da sai ya nemi taimako daga wani masani kan yadda ake gina shafin yanar gizo ba.

Haka kuma, mafi yawanci, akan samu wajen yin sharhi ko tsokaci ("comment") a kan kowane bayanin (kasida) da aka wallafa a shafin blog, abin da ke da matukar wuya a samu a daskararrun shafuka.

Sannan sau da yawa a shafin blog, an fi saukin samun mashigan tura duk wani kasida da aka samu daga shafin zuwa wasu shahararrun zaurukan zumunta irin su facebook da twitter, don gayyatan 'yan'uwa da abokai zuwa shafin da aka wallafa kasidan.

Kammalawa - Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata a Lura:
Duk wanda ya karanta bayanan da na kawo a sama, cikin nutsuwa, zai iya fahimtar cewa: shafin yanar gizo da shafin bulog kusan duk abu daya ne. Sai dai shi shafin blog kawai wani nau'i ne daga cikin nau'ukan shafin yanar gizo.

Don haka, ana iya kiran kowane shafin bulog da sunan "shafin yanar gizo" tare da lura da cewan nau'in sa shi ne "blog".

Ana iya samun shafin yanar gizon da ya kunshi bangarorin biyu, wato bangaren daskararrun shafuka masu kunshe da bayanai tsayayyu, da kuma bangaren blog wanda kan kunshi sababbin mashigai na shafuka masu dauke da sababbin bayanai.

Shawara:
Idan mutum na da burin mallakan shafin yanar gizo musamman na kamfani ko kungiya ko kasuwancin sa, to ina ba shi shawaran cewa ya yi kokari ya nemi kwararren maginin shafin yanar gizon da zai gina masa shafin yanar gizo wanda ya kunshi bangaren daskararren shafi da kuma bangaren blog. Domin hada duka biyun waje guda shi ke bayar da cikakken dama na saka kowane bayani a muhallin da ya dace da shi. Misali, mai shafi zai samu daman jero ayyukan sa ko hajojin sa a wani daskararren shafi da zai iya sanya wa taken "Ayyukan Mu" ko "Hajojin Mu", sannan kuma zai samu daman wallafa jerin sababbin hajoji ko labaran kamfanin sa ko kungiyan sa a wani shafi mai motsi da zai iya sanya wa taken "Blog" ko "Sababbin Hajojin Mu" ko "Meye Sabo?" ko "Labaran Mu" ko "Kasidu" da dai makamantan su.Shafin yanar gizo da kuma shafin blog wasu kalamai ne wadanda kusan duk wani ma'abocin amfani da fasahar intanet ya saba da jin su ko ganin su, sai dai a mafi yawancin lokuta, ba tare da sanin hakikanin ma'anonin su ko bambancin da ke tsakanin su ba. Fahimtan su na da matukan muhimmanci musamman ga wadanda ke son mallakan na su shafin a duniyar gizo. A wannan kasida zan yi kokarin yin takaitaccen bayani ne wanda na ke fatan zai gamsar da duk wani mai son sanin ma'anan shafin bulog da kuma bambancin su da shafin yanar gizo.

Ma'anar Shafin Blog
Shafin blog wanda kalma ne na harshen turanci da ya samo asali daga "weblog", shi ne shiryayyen shafin yanar gizo wanda aka kirkire shi a bisa tsarin da za a iya sabunta shi da bayanai akai-akai, cikin sauki. Ana kirkiran shafin blog ne da wani shiryayyen manhajar yanar gizo na musamman da ke bayar da daman kirkira da kuma gudanar da shafin bulog. Shafukan yanar gizo na mujalla da shafukan yanar gizo masu kawo labarai ko darussa, kaman wannan shafi na Duniyar Sadarwa, su ne misalan shafukan blog, wato su ne ire-iren shafukan da akan kirkire su a bisa manhajar yanar gizon kirkiran bulog.

Magina manhajar yanar-gizo wadanda a turance ake kira "web developers" ko "web programmers" su ne ke iya kirkiran manhajar bulog ta hanyar amfani da sababbin fasahohin zamani na kirkiran shafukan yanar gizo. Akwai kuma kamfanoni daban-daban a duniyar gizo wadanda ke dauke da irin wannan manhajar yanar gizon da ke bayar da daman kirkira da kuma gudanar da shafin blog. Mafi shahara daga ciki su ne: Blogger da Wordpress. Irin wadannan kamfanoni kan tsara manhajar su ne ta yadda idan mutum ya yi rajista a shafin su, zai samu tsararren shafin sa na blog kuma zai samu daman wallafa kasidu ('posts') da kuma yin gyare-gyare a shafin sa na blog din ta wani shiryayyen shafi da akan kira 'control panel' ko 'dashboard' a turance.

Babban dalilin da kan sa a bukaci shafin blog shi ne samun saukin wallafa bayanai na rubuce-rubuce ko fayiloli irin su hotuna da sautuka, akai-akai.

Samuwar fasahar blog a duniya, shi ya bude wa kamfanonin watsa labarai da makamantan su hanyar wallafa labarai a shafin yanar gizo cikin sauki da kuma sauri.

Irin tarin alfanun da fasahar blog ya kawo a duniyar gizo, shi ya janyo samun karbuwan sa ga al'ummomi daban-daban na sassan duniya.

Duk wani shafi da ke duniyar gizo, sunan sa shafin yanar gizo. Don haka Kowane shafin blog shafin yanar gizo ne amma ba kowane shafin yanar gizo ne shafin blog ba.

Wani babban abu da na ke ganin zai saukaka fahimtan bambanci tsakanin shafin blog da shafin yanar gizo, shi ne a sani cewa dole ne duk wani shafi da ke duniyar gizo zai kasance mai nau'i daya daga cikin nau'uka guda biyu na shafin yanar gizo: Shafin yanar gizo mai motsi da kuma shafin yanar gizo mare motsi.

Shafin yanar gizo mai motsi shi ne shafin da aka shirya shi musamman da nufin a rika sabunta shi da bayanai akai-akai, a saukake, kuma a mafi yawancin lokuta, shi ne ake yi wa lakabi da "shafin blog" ("weblog"). Sai dai idan ana batun "shafuka masu motsi" a jimlance, to za a hada har da shafukan sada zumunta irin su twitter da facebook.

Shi kuma shafin yanar gizo mare motsi shi ne shafin da ke dauke da wasu bayanai tsayayyu. Ma'ana ba shafi ne da aka gina shi da nufin a rika sabunta shi da sababbin bayanai akai-akai ba. A kan yi masa lakabi da "daskararren shafi", amma a mafi yawancin lokuta, ba a cika yi masa wani lakabi ba, sai dai kawai a kira shi da "shafin yanar gizo" ("website") tunda shi ne nau'in shafin yanar gizon da duniya ta sani kafin fitowan fasahar bulog.
No comments:
Write Comments