Home YADDA AKE KIR_KIRAN {TEXTBOX} AKOWANI IRIN BLOG

Akwatin rubutu (ko 'textbox' a turance), wani salo ne da magina shafin yanar gizo kan yi amfani da shi don bai wa masu mu'amala da shafin daman yin rubutu a ciki (domin cike fom) ko kuma daukan rubutu daga ciki a shafin yanar gizon. Kusan duk wani shafin yanar gizo da ke bayar da daman cike wani fom a shafin, to dole zai kasance akwai akwatin rubutu. Misali, idan za a yi sharhi (comment) a kan wannan darasin, ko za a aiko da sako a wannan shafin, to za a yi amfani da akwatin rubutu ne wajen rubuta abin da ake son aikawa, sannan bayan an rubuta sai a latsa maballin aikawan.
Sai dai kamar yadda na ambata a farko, ba a wajen cike fom ko aikewa da sako ne kadai ake amfani da akwatin rubutu ba. A lokuta da yawa, masu tafiyar da shafin yanar gizo ko blog kan bukaci sanya wani rubutu ko kod cikin irin wannan akwatin rubutu don bai wa maziyarta shafin su daman dauka ko kwafe rubutun ko kod din daga ciki a saukake ta hanyar yin "copy" zuwa "clipbord" na manhajar shiga intanet din su, ta yadda daga nan za su samu damar ajiye shi (paste) a inda su ke bukata. Wannan shi ne abin da wannan darasi zai koyar, don amfanar masu tafiyar da shafin yanar gizo ko bulog.

Yadda Za a Kirkiri Akwatin Rubutu a Kowane Irin Shafin Yanar gizo Ko Blog

Ana amfani da wani kod na HTML ne don kirkiran akwatin rubutu a kowane irin shafin yanar gizo ko kuma blog. Ga kod din:
<*p><*textarea cols="20" rows="5"> Rubutun ko kod a nan... <*/textarea><*/p>
Kar a manta: a cire alamun * daga kod din kafin a yi amfani da shi. Sannan a lura da wajen da aka sa " Rubutun ko kod a nan... ", nan za a goge, sai a rubuta abin da ake so ya kasance cikin akwatin.

Yadda Za a Canja Girman Akwatin Rubutun

Ana iya karawa da kuma rage fadi ko tsawon akwatin rubutun zuwa dai-dai yadda ake bukata. Idan an dubi kod din na kirkiran akwatin rubutu, za a ga wajen da aka sacols="20" da kuma rows="5". To wadannan bangarori biyu na nufin fadi da kuma tsawon akwatin rubutun. Don haka idan ana so a canja fadin sai a canja lamban na 20 zuwa wani lamba na dai-dai fafin da ake so. Haka idan ana son canja tsayin akwatin rubutun, sai a canja lamban 5 zuwa wani lamban na dai-dai tsayin da ake so.
Karshen wannan darasin ke nan, sai kuma mun hadu a darasi na gaba da yardan Allah. Amma kafin nan, ina fatan an fahimta kuma an amfana kuma an ji dadin wannan.
No comments:
Write Comments