Home YADDA AKE BUDE GOOGLE ACCOUNT {GMAIL}


A Sashin Harkokin Duniyar Gizo

new-google-gmail-inbox.png
Gmail ya na da saukin budewa da kuma karanta sako ko aikawa a wayar hannu. Idan ka na so ka mallaki naka Gmail din a yanzu, to kawai ka bi wadannan matakan.

1- Da farko ka shiga www.gmail.com . Za ka ga wajen da aka sa 'New to Gmail? It's free and easy. Create account'. To sai ka danna 'Create account'.

2- Zai budo maka wajen da za ka zabi sunan kasar ka. (country) da kuma wajen da za ka rubuta lambar wayar ka. To a wajen 'choose country', za ka ga 'change' sai ka danna shi.

select-change.jpg
Zai jero maka haruffa, sai ka zabi harafin da sunan kasar ka ya fara da shi. misali, 'N' idan a Nigeria ka ke ko Niger.

nigeria.png
Bayan ka zabi sunan kasar ka, zai dawo da kai wajen da za ka saka lambar wayar ka. To sai ka dan yi kasa kadan, sai ka rubuta lambar wayar da ka ke kan amfani da shi a wayar ka a yanzu. Sai ka danna 'Next'.

3- Za su aiko sakon SMS ga lambar da ka sa, cikin yan mintunan da basu wuce 15 ba. Sai ka dan jira kadan, da zaran sakon ya shigo, sai ka je inbox din ka, ka bude. A cikin sakon, za ka ga wani adireshi (link), sai ka latsa wannan link din. Ko kuma ka kwafe shi, sai ka je browser din ka, ka shiga ta ciki.

4- Bayan ka latsa link din, ya bude, za ka ga wani fom da za ka cike sunan ka (first name), sunan mahaifi (last name) ranar haihuwa (date of birth), da kuma jinsi (gender). Bayan ka cike, sai ka danna 'Next'.

5- Zai budo maka wajen da za ka zabi 'Username' din ka wato sunan da zai zamo adireshin Email din ka. Za ka ga sun baka wasu misalan sunayen adirishin da za ka iya zaba a kasa. Idan kuma wani daban ka ke so, ba daga cikin wadannan da suka baka ba, to sai ka rubuta wanda ka ke so. Da ka rubuta sai ka danna 'Next'. Amma idan akwai wani mai irin wannan sunan, to za su ce bai karbu ba. Ka sake canza wani.

6- Zai budo maka wani shafi da za ka saka mabudin ka na sirri (password). Sannan ka sake maimaita shi a kasa (retype password). Sai ka danna 'Finish'. Shi kenan! Ka gama bude sabon adireshin E-mail din ka na Gmail!

A lura cewa, yana da kyau a yi amfani da browser na Opera-mini ko kuma ainihin browser na wayar yayin yin wannan rajista. Amma ba Uc-browser ba.
Bi wadannan matakai guda shida da muka kawo a yanzu ciki nutsuwa, domin bude sabon adireshin e-mail din ka/ki na Gmail daga wayar hannu.

Idan akwai tambaya sai a yi comment!

No comments:
Write Comments