Home YADDA KE TURA SAKO TA EMAIL ADDRESS {GMAIL}

A baya, mun yi cikakken bayani game da yadda ake bude sabon adireshin Email na Gmail a wayar hannu. Da fatan duk wanda ba shi da Email na Gmail, a yanzu ya mallaki nasa. Idan kuma akwai

mai tambaya, ko kuma akwai wani abu da ba a fahimta ba game da bayanin da muka yi, to ana iya yin comment.

Yanzu kuma, za mu yi bayani ne a takaice, kan yadda mai amfani da Gmail zai aika sako daga Email din sa zuwa ga wani.

Wannan abu ne mai sauki da ba ya bukatar wani dogon bayani.

Domin aika sakon Email daga Gmail din ka kawai abin da za ka yi shi ne,

* Ka bude gmail din ka (wato ka yi login) tare da email din ka da password ta shafin www.gmail.com .

* Idan ya bude sai ka nemi inda aka sa 'Compose' sai ka danna.

* Zai budo maka wani shafi.

* To, a wajen da ka ga an sa 'To' anan ne za ka rubuta adireshin Email din wanda za ka aika ma sakon.

* Wajen da aka sa 'Subject' kuma a nan ne za ka rubuta 'maudu'in sakon'.

* Sai ka yi kasa, ka rubuta wasikar ka a akwatin da aka tanadar, wato wajen da aka sa 'Message'.

* Da ka gama sai ka danna 'SEND'. Shikenan! Nan take sakon zai tafi zuwa Inbox din wanda ka aika ma.

P
No comments:
Write Comments