Home Daga kamfanin WhatsApp

Kamfanin WhatsApp a watannin baya ya fitar da wani labari da ke cewa adadin masu amfani da manhajar WhatsApp ya kai miliyan dari biyar (500,000,000). Inda a yanzu adadin ya haura zuwa sama da miliyan dari bakwai (700,000,000). A dai-dai lokacin da masu amfani da manhajar na WhatsApp ke ta karuwa a sassa daban-daban na duniyar, wani labari mai kayatarwa ga masu amfani da manhajar na WhatsApp da muka samu a satin da ya gabata, shi ne labarin fitowar sabon tsarin yin kira a WhatsApp din. Masu amfani da WhatsApp da dama a yanzu suna iya kiran junan su kyauta ta hanyar amfani da 'data' na Intanet. Wato dai a takaice, kamar yadda manhajar Viber ya ke. Sai dai kuma masu amfani da WhatsApp a wayoyin Android ne kadai ke da daman samun wannan sabon tsari a yanzu.

1 comment:
Write Comments