YADDA ZAKA SAMU 50mb KULLUM

Assalamu alaikum barankan mu da kasancewa awannan lokaci yauma kamar kullum muna dauke da hanyar da zakuna samin 50mb daily (kullum) Kar in cikaku da surutu bari muje CIKIN darasin kai tsaye Dafari ku dauko wannan app din  https://m.apkpure.com/stark-vpn-reloaded-new-stark-vpn/istark.vpn.starkreloaded wasun ku Susan wannan app din wasu kuma suma dashi amma yadena aiki to wannan guarantee ne bayan kun dauko sai kuyi install dinsa bayan kunyi sai ku bude shi zai nunamuku kamar hakabayan yamuna muku wannan sai ku danna digo digonna 3 daya ke hanun damanku zai nuna muku wani guri kamar haka
bayan yanuna muku kamar haka sai ku danna back bayan yadawo daku farkon app din saiku danna inda aka rubuta CUSTOM bayan kun danna zai nuna muku kamar haka bayan yanuna muku kamar haka sai ku danna na uku inda aka rubuta  mtn 50 mb daily bayan kun danna zai  dawo daku farkon sai ku danna jan round dinna da aka rubuta DISCONNECTED dinna sai kujira yanuna muku kamar haka yana nunamuku kamar haka to Shikenan sai afara morar datan Kar a manta bude data kafin a shiga CIKIN app din.

Bissalam duk Wanda bai gane ba ko yana bukatan Karin bayani zai iya ajiyewa a comment karku manta saka email din ku gurin yin subscribe don samun darussanmu da dumi duminsu in munyi sabon post 

DAGA NAKU HARKULLU IBRAHIM MUSA GM (ibsoon gee)  (Mr no name) 

YADDA AKE TARA SAMA DA 2GB DA MY MTN ARANA

 
Assalamu alaikum barkan mu da arzikin Kara saduwa acikin wannan Dandali namu mai al barka. Yauma kamar kullum muna dauke da hangar da mutum zai Tara SAMA da 2gb a rana  da my mtn kar dai nacikaku dasurutu da fari ya kamata fara sauke my mtn in baka dashi a wayanka sai ma danna nan domin yin downloading dinsa https://m.apkpure.com/mymtn/com.mtn1app bayan kayi downloading dinsa sai ka bude shi bayan kabude shi zai nuna maka kamar hakabayan yanunamaka kamar haka sai ka danna kan arrow nan wato invite&get free Data bayan yabude zai Kara kaika guri kamar hakabayan ya nunama box guda 5 sai kasa numbers na abokanayenka KO na wanada ka keso kayi invite bayan kasa numbers din sai ka danna inda arrown nan yanunabayan kun latsa sent invite to sai ku karbi wayan duk Wanda katurawa invite sai katura masa my mtn KO yayi download dinsa dazaran yabude zasu bashi kyutan data 500 KO 100 kai kuma kowani mutum daya in yabude my mtn India katura masa inviting to za abaka 200 data kaga mutum biyar zai Kama 1g mutum 10 2gb. Allah yabada sa, a


Daga naku masoyinku Ibrahim musa GM Wanda kukafi sanida ibsoon (Mr no name) 

YADDA AKE HADA PHOTOS APPLICATION DA WAYAR ANDROID

ASSALAMU ALAIKUM Barkan muda warhaka Barkan muda sake kasance acikin wanna web side mai albarka. 
Batare da wani  bata lokaci ba zan nunamuku yadda ake create PHOTOS APP da fari ku shiga nan kuyi  download din app din https://m.apkpure.com/apk-creator/com.gmail.heagoo.apkcreator bayan kunyi download dinsa sai kuyi install dinsa bayan kunyi install dinsa sai ku budeshi zai nuna muku kamar hakabaya yabude saiku danna creat a picture apk bayan kun danna sai Kara kaiku shafi nagaba kamar haka inda akasa app name sai kusa sunan app din ku guri app icon sai kusa photon da kuke so yafito a kan app din ku guri cover image sai kusa photon dazai fito a back ground din app din bayan kunsa gurin image colums sai kusa yawan yadda kuke son group group na photunan gida nawa kuke son su kasu bayan kusa zakuga picture group 1 one sai kidanna kan  plus ➕ dinnan bayan kun danna zai kai ku cikin photunan ku sai kuzabi wadda kuke son su kasance a group din in kun gama zaba sai ku danna create apk daganan sai kudan jira yana gamawa zai nuna muku kuyi install din shi bayan kunyi install dinshi daga nan sai ku bude shi zakuga app dinku ya kammala. Mai tambaya zai iya iyi ta comment. 
DAGA NAKU HARKULLUM IBRAHIM MUSA GM ( ibsoon gee). 
Karku manta saka email dinku guri yin subscribe domin samun sababbin post din mu akan lokaci mungode da ziyarta shafin mu. 

YADDA AKE SAMUN FREE MB TA FLAIM APP

 
Assalamu alaikum barkanku da warhaka barkammu da zuwa internethausa batare da bata lokaciba zan muku bayani wani app da zaku tara megabyte mb iya son ranku dafari kufara dauko app din tawannan link din https://m.apkpure.com/flaim/equiis.flaim.im bayan kunyi downloading dinsa sai kuyi install din sa bayan yagama sai ku bude shi zai nuno muku kar hakabayan yanuna muku sai kudan jira bayan kamar 10sc zai bude bayan ya bude zai nuna muku Wani page kamar hakabayan ya nuna muku haka Sai kudanna kan Get started bayan kun danna zai Kara kai ku Wani page kamar hakabayan ya bude Sai kusa number wayan ku kutabbata layin yana kan wayan ku bayan kunsa numbernku Sai kudanna send verification code bayan kun danna zai Kara kai ku Wani page kamar haka bayan ya nuna muku haka Sai ku jira zasu turomuku verification code numbobi 8 bayan sun turo muku Sai kumaida sabis din wayan ku 2g in 4g ne KO 3g bayan kun maida shi saikusa numbobin da Suka turo muku Kuna sawa zai nunomuku yana verify kar kubari yagama verify  Sai ku danna back har Sai yadena verify zakuji massage Kuna dubawa zakuga sun baku mb 75 to Sai ku Kara dawowa cikin FLAIM kukara sa verification code dinna namma kafun yagama kudanna back haka zaku tayi suna baku 75mb amma fa in kuka bark yagama verify to shikenan kungama Cin bonanzan. Duk mai tambaya zai iya min ta comment karku mata yi subscribe domin samun sabbin post din mu. 
Daga naku IBRAHIM MUSA GM (ibson gee) 

YADDA AKE HADA APK

 

KODULAR CREATOR: kodular creator shima kamar appybuilder ne saboda shima yana cikin family din drag and drop ne, idan ka iya appybuilder baka da bukatar koyon kodular haka kuma idan ka iya kodular baka da bukatar koyon appybuilder . kusan komai nasu daya ne, sai dai extension ko source code na kodular baya yi a appybuilder hakanan kuma na appybuilder baya yi a kodular kuma ba zaka iya bambancewa ba saboda duka source codes dinsu yana karewa da .aia ne, haka kuma duka extension nasu yana karewa da .aix ne don haka duk wanda ya baka extension ko ka saya to dole ya gaya maka na wane portal ne, saboda idan kayi uploading zai hau portal din amma ba zai yi ba kuma ba zai ce maka wai ba nasa bane ba.

Amfanin kodular da appybuilder kusan duk daya ne, dan bambancin shine kodular yafi dadin sha’ani ga wanda ya fahimce shi, amma appy builder yafi sauki ga dan koyo. Abu na biyu kodular sun fi appybuilder cpc mai kyau. Abu na uku su kodular ba’a iya hada earning app da su wato application wanda baya containing komai sai ads. Shi yasa idan ka kammala app da su to tilas sai kayi requesting for review sun tantance sannan ya fara nuna ads.

Sannan kuma suna da wata illa daya bayan ka gama building apps dinka to tilas ka saurara minimum of 48 hours sannan kayi requesting review amma idan publishing zaka yi a playstore to ba sai jira ba, kawai kayi publishing duk da baya nuna ads din, da zaran ya shiga playstore zai fara nunawa.

Domin jarabawa shiga nan KODULAR


APPYBUILDER: appybuilder ma wani portal ne da ake amfani da shi wajen hada app wanda zaka iya kusan duk wani app da ka sani ta hanyar amfani da shi. Appybuilder da duk sauran portals ire-iren shi ana kiran su drag and drop portals saboda su zaka rika dragging and dropping na feature ne kawai daga baya sai kayi compiling.
Appybuilder ya sha bambam da duka sauran portals din da muka ambata tun daga tsari da yanayi da kuma yanayin aiki. Sannan shi appybuilder kyauta ne ake amfani da shi zaka iya monetizing app din ka fully ta hanyar nuna banner da interstitial ads a app dinka kuma zaka iya customizing package name na app dinka yadda kake so.

AMFANINSU
Kyauta ne gaba daya babu wani subscription.
Zaka iya importing na wani feature wanda basu da shi ta hanyar amfani da extension files.
Zaka iya amfani da souce code kawai kayi editing ka sanya details naka.
Zaka iya publishing app dinka a playstore.
 Suna da saukin sha’ani musamman idan apps din ka masu saukin building ne.

ILLOLINSU
§ Duk earning din ka na google suna da 5% shi yasa ba zaka iya using dinsu ba dole sai da gmail.
§ Idan kana bukatar extension to ba duka bane suke bayarwa free dole ka saya akan kudi mafi karanci dala 10.
§ Suna da low cpc.
§ Wasu apps dinsu google basa yarda ayi publishing dinsu a playstore misali earning apps.
Shiga nan don jarabawa APPYBUILDER

APPYPIE: shima wani portal ne wanda ake creating android apps ko iphone kai har ma da Windows apps su kuma usually suna baka tsawon sati biyu ne ka jaraba amfani dasu a kyauta wanda bayan sati biyun nan ya wuce to ba zaka iya cigaba da amfani da su ba har sai kayi subscription. Gaskiya suna da features masu kyau, zaka iya yin apps masu kyau sama da kala dari masu ban sha’awa.

AMFANINSU
Suna features masu kyau don features dinsu yafi na andromo kyau.
Suna supporting different apps kamar irin su website apps, ebook, notebooks da sauransu.
Zaka iya publishing na apps dinsu a playstore.
Suna da push notification feature wanda zaka iya tura ma duk wanda yayi installing na app dinka message. Wannan feature din sune kadai suke das hi a duk cikin portals da muka lissafa.

ILLOLINSU
Suna da yar wuyar sha’ani ga dan koyo ba kamar appsgeysa da andromo ba.
Site dinsu is not mobile friendly, ma’ana idan ba da PC kake using ba to gaskiya zai rika yi maka slow ne

Ku shiga nan don jarabawa APPSGEYSER

: andromo yana cikin manya kuma shahararrun portals da ake amfani da su wajen creating applications irin na wakoki, ebooks, website, rubutun zube da sauransu. Kusan ince kowa zai iya developing application a Andromo. Da farko zaka yi register da su, daga nan zasu baka dama kayi creating application daya don kaga yadda suke da saukin sha’ani. Bayan kayi creating wannan app din kwara daya ba zasu baka dama ka sake creating wani ba har sai kayi subscription da su saboda su services nasu ba kyauta bane. Zaka rika biyansu akalla dala 8 duk wata kuma basa accepting subscription na wata daya, karanci shekara daya ne. kaga kenan zaka yi lissafin dala takwas sau 12 sune adadin kudin da zaka biya su don more amfani da portal nasu.

AMFANINSU
Suna da matukar saukin sha’ani.
 Zaka iya amfani da emails daban-dban don sake register don more garabasar app daya da suke bayarwa.
Shi app dayan zaka iya updating dinsa ta hanyar cire content dinsa kacokan ka sanya wani content din.
Apk dinsu is highly compressed bjarabawa nauyi ba.
Apps dinsu yana da cpc mai kyau.

ILLOLINSU
Idan baka yi subscription da su ba, to ba zasu baka damar sanya admob ad units dinka ba.
Basa karbar subscription na wata daya sai akalla ya kai na shekara.
Suna sanya watermark a free apps dinsu, wato alamar cewa a wajen su ne kayi app din.
Idan subscription dinka na dala 8 ne a wata to ba zaka iya customizing package name naka yadda kake so ba.
Shiga nan don jarabawa

YADDA AKE SAWA FACEBOOK SECURITY system

wani tsarine da facebook suka bawa masu amfani da shafinsu wata dama wanda xaka kare facebook dinka ta hanyar sanya masa security shi wannan tsari yana da matukar dadi sannan kuma yana da mungun hadari domin kuwa dakayi active na wannan tsarin to facebook xasu turoma da text wanda yake dauke da security wannan security to shine abu mai muhimmanci wanda da shine idan kayi login na account din to xa,a umar ceka kasa pin dinka to dole saikasa wannan security sannan xai bude to ka ga kwa babu dama wani yahau fb dinka domin idan yahau xasu umarci yasa pin to matsalar sa kuma shine idan har ka manta wannan security da suka baka to sai ince ta karema domin babu dama kahau fb dinka saide yanxu koda ka manta paswod din idan kahau wata operar kayi login to xasuyi text xuwa number ka da new security to sai kaje kasahi sannan ya bude Ina sake nana ta muku yana da hadari da xarar ka seta idan sim din ya bata to babu kai babu hawa facebook Sabo da haka akiyaye to baride mu fara bayanin kaje facebook dinka ta opera ka budeshi sannan kayi chan kasa xakaga inda aka rubuta to saika shiga nan idan ya bude xakaga abubuwa A Jere Kamar Haka …… GENARAL SECURITY PRIVESY TIMELINE & TAGGING BLOCKING NOTIFICATION TEXT MESSAGING To Kawai Saika Shiga Idanya Bude To Zakuga kai tsaye ya bude muku wuri kamar haka … inda Idan Kuka Lura Zakuga Jerin Sunaye Guda Uku Na Farko .. 1= Text message login Code .. Enable 2= Login Notification code .. Enable 3= Login Aproval ON .. Enable To Anan Abinda Ake Bukata Shine Duka Anason Sai Mun Maida Enable ta koma Deable.. Tashin Farko Domin Saita na tsakiya domin shiyafi saukin saiti watoEmail Notification login Code kawai saika danna kalmarEnableinda zakaga nan take ta canja kanta daka enable zuwa kalmar Disable.. Amfanin saita wannan kuwa shine Aduk lokacin da wani hatsa bibi yayi yunkurin hawa Facebook dinka tonan take Facebook zasu sanar dakai ta hanyar sakon message zuwa Akwatin email dinka … Suma sauran su Text message login code da Login Aproval to suma haka xaka musu wato ka maidasu dan enable xuwa denable idan kayi haka shikkenan duk lokacin da wani yayi kokarin hawa account dinka to xasu sanar dakai cewa xa a hau fbok dinka da opera kaxa da waya kaxa kuma a time kasa sannana xasu turoma da wani new security domin ka yi amfani dashi kuma ko kaine xakahau fb din naka a wata wayar to sai sun ma hakan Allah ya bada sa,a

BAN_BANCIN BLOG DA WEBSITE

 
Bambance-bambancen Da Ke Tsakanin Shafin Yanar Gizo Da Shafin Blog
Babban abin da ya bambanta daskararren shafi da kuma shafin blog shi ne yanayin yadda bayanan shafin ke kasancewa. Shi shafin blog kan kunshi bayanai ne a bisa tsarin daya na-biye da daya, sabon bayani a saman tsohon bayani, sannan kowanne na dauke da lokaci ko kwanan watan da aka wallafa shi da kuma sunan wanda ya wallafa shi. Yayin da shi kuwa daskararren shafi, bayanan sa tsayayyu ne a bisa tsarin da maginin shafin ya gina su. Idan ana son sauya su, to za a tuntubi maginin shafin ne domin sai an bukaci yin gyara ko kari a cikin kod din da aka gina shafin da shi. Anan, za a iya fahimtar cewa shafin blog na saukaka wa mai shi daman wallafa sababbin bayanai da kan shi, ba tare da sai ya nemi taimako daga wani masani kan yadda ake gina shafin yanar gizo ba.

Haka kuma, mafi yawanci, akan samu wajen yin sharhi ko tsokaci ("comment") a kan kowane bayanin (kasida) da aka wallafa a shafin blog, abin da ke da matukar wuya a samu a daskararrun shafuka.

Sannan sau da yawa a shafin blog, an fi saukin samun mashigan tura duk wani kasida da aka samu daga shafin zuwa wasu shahararrun zaurukan zumunta irin su facebook da twitter, don gayyatan 'yan'uwa da abokai zuwa shafin da aka wallafa kasidan.

Kammalawa - Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata a Lura:
Duk wanda ya karanta bayanan da na kawo a sama, cikin nutsuwa, zai iya fahimtar cewa: shafin yanar gizo da shafin bulog kusan duk abu daya ne. Sai dai shi shafin blog kawai wani nau'i ne daga cikin nau'ukan shafin yanar gizo.

Don haka, ana iya kiran kowane shafin bulog da sunan "shafin yanar gizo" tare da lura da cewan nau'in sa shi ne "blog".

Ana iya samun shafin yanar gizon da ya kunshi bangarorin biyu, wato bangaren daskararrun shafuka masu kunshe da bayanai tsayayyu, da kuma bangaren blog wanda kan kunshi sababbin mashigai na shafuka masu dauke da sababbin bayanai.

Shawara:
Idan mutum na da burin mallakan shafin yanar gizo musamman na kamfani ko kungiya ko kasuwancin sa, to ina ba shi shawaran cewa ya yi kokari ya nemi kwararren maginin shafin yanar gizon da zai gina masa shafin yanar gizo wanda ya kunshi bangaren daskararren shafi da kuma bangaren blog. Domin hada duka biyun waje guda shi ke bayar da cikakken dama na saka kowane bayani a muhallin da ya dace da shi. Misali, mai shafi zai samu daman jero ayyukan sa ko hajojin sa a wani daskararren shafi da zai iya sanya wa taken "Ayyukan Mu" ko "Hajojin Mu", sannan kuma zai samu daman wallafa jerin sababbin hajoji ko labaran kamfanin sa ko kungiyan sa a wani shafi mai motsi da zai iya sanya wa taken "Blog" ko "Sababbin Hajojin Mu" ko "Meye Sabo?" ko "Labaran Mu" ko "Kasidu" da dai makamantan su.Shafin yanar gizo da kuma shafin blog wasu kalamai ne wadanda kusan duk wani ma'abocin amfani da fasahar intanet ya saba da jin su ko ganin su, sai dai a mafi yawancin lokuta, ba tare da sanin hakikanin ma'anonin su ko bambancin da ke tsakanin su ba. Fahimtan su na da matukan muhimmanci musamman ga wadanda ke son mallakan na su shafin a duniyar gizo. A wannan kasida zan yi kokarin yin takaitaccen bayani ne wanda na ke fatan zai gamsar da duk wani mai son sanin ma'anan shafin bulog da kuma bambancin su da shafin yanar gizo.

Ma'anar Shafin Blog
Shafin blog wanda kalma ne na harshen turanci da ya samo asali daga "weblog", shi ne shiryayyen shafin yanar gizo wanda aka kirkire shi a bisa tsarin da za a iya sabunta shi da bayanai akai-akai, cikin sauki. Ana kirkiran shafin blog ne da wani shiryayyen manhajar yanar gizo na musamman da ke bayar da daman kirkira da kuma gudanar da shafin bulog. Shafukan yanar gizo na mujalla da shafukan yanar gizo masu kawo labarai ko darussa, kaman wannan shafi na Duniyar Sadarwa, su ne misalan shafukan blog, wato su ne ire-iren shafukan da akan kirkire su a bisa manhajar yanar gizon kirkiran bulog.

Magina manhajar yanar-gizo wadanda a turance ake kira "web developers" ko "web programmers" su ne ke iya kirkiran manhajar bulog ta hanyar amfani da sababbin fasahohin zamani na kirkiran shafukan yanar gizo. Akwai kuma kamfanoni daban-daban a duniyar gizo wadanda ke dauke da irin wannan manhajar yanar gizon da ke bayar da daman kirkira da kuma gudanar da shafin blog. Mafi shahara daga ciki su ne: Blogger da Wordpress. Irin wadannan kamfanoni kan tsara manhajar su ne ta yadda idan mutum ya yi rajista a shafin su, zai samu tsararren shafin sa na blog kuma zai samu daman wallafa kasidu ('posts') da kuma yin gyare-gyare a shafin sa na blog din ta wani shiryayyen shafi da akan kira 'control panel' ko 'dashboard' a turance.

Babban dalilin da kan sa a bukaci shafin blog shi ne samun saukin wallafa bayanai na rubuce-rubuce ko fayiloli irin su hotuna da sautuka, akai-akai.

Samuwar fasahar blog a duniya, shi ya bude wa kamfanonin watsa labarai da makamantan su hanyar wallafa labarai a shafin yanar gizo cikin sauki da kuma sauri.

Irin tarin alfanun da fasahar blog ya kawo a duniyar gizo, shi ya janyo samun karbuwan sa ga al'ummomi daban-daban na sassan duniya.

Duk wani shafi da ke duniyar gizo, sunan sa shafin yanar gizo. Don haka Kowane shafin blog shafin yanar gizo ne amma ba kowane shafin yanar gizo ne shafin blog ba.

Wani babban abu da na ke ganin zai saukaka fahimtan bambanci tsakanin shafin blog da shafin yanar gizo, shi ne a sani cewa dole ne duk wani shafi da ke duniyar gizo zai kasance mai nau'i daya daga cikin nau'uka guda biyu na shafin yanar gizo: Shafin yanar gizo mai motsi da kuma shafin yanar gizo mare motsi.

Shafin yanar gizo mai motsi shi ne shafin da aka shirya shi musamman da nufin a rika sabunta shi da bayanai akai-akai, a saukake, kuma a mafi yawancin lokuta, shi ne ake yi wa lakabi da "shafin blog" ("weblog"). Sai dai idan ana batun "shafuka masu motsi" a jimlance, to za a hada har da shafukan sada zumunta irin su twitter da facebook.

Shi kuma shafin yanar gizo mare motsi shi ne shafin da ke dauke da wasu bayanai tsayayyu. Ma'ana ba shafi ne da aka gina shi da nufin a rika sabunta shi da sababbin bayanai akai-akai ba. A kan yi masa lakabi da "daskararren shafi", amma a mafi yawancin lokuta, ba a cika yi masa wani lakabi ba, sai dai kawai a kira shi da "shafin yanar gizo" ("website") tunda shi ne nau'in shafin yanar gizon da duniya ta sani kafin fitowan fasahar bulog.